in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta jajirce wajen kiyaye makamashin nukiliya bisa tsari da daidaito
2017-09-19 10:08:47 cri

Kasar Sin ta dauki matakan kiyaye ka'ida da daidaito a matsayin dabarun inganta makamashin nukiliya a kasar.

Shugaban tawagar kasar Sin a wajen taro na 61 na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Tang Dengjie ne ya bayyana haka a jawabinsa na bude taro da aka yi a Vienna.

Tang Dengjie wanda shi ne shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar Sin kuma mataimakin ministan masana'antu da fasahar sadarwa, ya ce kasar Sin ta rungumi matakan ne domin inganta samar da makamashin nukiliya bisa dabarum tsaro da kiyayewa.

Ya ce, sabuwar dokar tsaron nukiliya da majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin ta samar a farkon watan nan, zai ba da cikakken goyon baya ga tsaro da dorewar inganta makamashin nukiliya a kasar.

A yanzu haka, kasar Sin na da na'urorin sarrafa makamashin nukiliya guda 36, inda kuma take kokarin samar da wasu karin 20. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China