in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira ga kasa da kasa da su martaba yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya
2017-05-03 10:59:54 cri
A jiya Talata ne wakilin kasar Sin mai kula da harkar kwance damara, Mr. Fu Cong ya bayyana a birnin Vienna cewa, kamata ya yi gamayyar kasa da kasa su martaba yarjejeniyar da aka cimma game da hana yaduwar makaman nukiliya. A wannan rana, an gudanar da taron share fagen babban taron nazarin yarjejeniyar hana makaman nukiliya karo na 10 da za a gudanar a shekarar 2020, kuma kasashe 110 da suka daddale yarjejeniyar, ciki har da Sin da Amurka da Rasha da Birtaniya da kuma Faransa wadanda ke da makaman nukiliya, sun tura tawagoginsu wajen taron. Mahalarta taron dai za su tattauna kan yadda ake aiwatar da ayyukan kwance damarar makaman nukiliya da hana yaduwar makaman nukiliya da kuma bunkasa makamashin nukiliya cikin lumana, tare da shirya ajandar taron da za a gudanar. A jawabin da ya gabatar a yayin babbar muhawarar, Mr. Fu Cong ya yi nuni da cewa, yadda za a taimaka wajen kwance damarar makaman nukiliya ya zama babban batun da dole a yi la’akari da shi sosai a inda ake nazarin yarjejeniyar da za a gudanar a wannan karo. Ya kara da cewa, kullum kasar Sin na nuna hakikanin goyon bayanta ga aikin kwance damarar makaman soja tare kuma da kiyaye tsarin hana makaman nukiliya, haka kuma tana kokarin ganin an bunkasa makamashin nukiliya. (Lubabatu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China