in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a martaba yarjejeniyar nukiliyar Iran, in ji mataimakin shugaban kasar
2017-09-10 13:22:40 cri
Mataimakin shugaban kasar Iran, kana shugaban hukumar makamashin nukiliyar kasar Ali Akabar Salehi ya bayyana cewa, kasar Iran za ta ci gaba da martaba yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma, muddin su ma bangarorin da abin ya shafa za su ci gaba da martaba yarjejeniyar sau da kafa. Ko da yake, a halin yanzu, kasar Amurka ta ce mai iyuwa ne za ta janye daga wannan yarjejeniya.

A jiya ne, gidan talabijin na kasar Iran ya ruwaito Mr. Salehi na cewa, idan har kasar Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukuliyar kasar Iran, sauran kasashe da suka hada da Burtaniya, Jamus, Faransa, Sin da kuma Rasha za su ci gaba da martaba wannan yarjejeniya, kasar Iran ita ma za ta ci gaba da martaba wannan yarjejeniya da aka kulla.

Tun bayan da ya hau mukamin mulki ne shugaba Trump yake matsawa Iran lamba. Baya ga kin kawar da takunkumin da aka kakabawa kasar Iran, ya kuma ci gaba da kara mata wani takunkumi a fannoni daban daban.

Haka zalika, shugaba Trump ya taba sanar da ficewar kasar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, amma wasu jami'an gwamnatin kasar da suka hada da sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson, da takwaransa na tsaron kasar James Mattis da dai sauransu sun taka masa birki kan wannan mataki

Wannan mataki dai ya haddasa illa kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Iran, domin har yanzu wasu kamfanonin kasashen yamma suna shakkar ko za su zuba jari a kasar Iran, ko a'a. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China