Rahotanni na cewa, a halin yanzu, an shiga wani sabon zamani na bunkasuwar makamashin nukiliya a kasar Sin, ya zuwa shekarar 2020, adadin wutar lantarki da na'urorin nukiliya za su samar zai kai megawatts miliyan 88. Haka kuma, fasahohin kasar Sin na samar da wutar lantarki da makamashin nukiliya sun kasance a kan gaba a fadin duniya, lamarin da ya baiwa kasar Sin damar kasancewa cibiyar ayyukan samar da wutar lantarki da makamashin nukiliya a duniya. (Maryam)