in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta gargadi Amurka game da shiga harkokin hukumar IAEA
2017-08-27 14:05:10 cri
Jami'an Iran sun bukaci hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, kada ta bada kai ga matsin lambar da Amurka ke yi dangane da yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma a shekarar 2015.

A jiya Asabar ne kafofin yada labaran Iran suka ruwaito Ministan harkokin wajen kasar Javad Zarif na cewa, duk wani yunkurin Amurka na matsawa hukumar IAEA lamba dangane da nukiliyar Iran ya sabawa yarjejeniyar.

A ranar Juma'a da ta gabata ne, wakiliyar Amurka a MDD Nikki Haley ta ce Amurka na goyon bayan hukumar wajen amfani da dukkan iko wajen bibiyar shirin nukiliyar Iran.

Nikki Haley, ta ce hukumar mai hedkwata a Vienna na da kwarraru da kuma shirin sanya ido mai karfi a Iran. Sai dai, hukumar ba ta da damar ganin dukkanin shirin nukiyar kasar.

A jiya Asabar ne kuma wani mamba a kwamitin tsaro da harkokin kasashen waje na majalisar dokokin Iran Alireza Rahimi, ya ce matsain lambar da Amurka ke wa hukumar IAEA dangane da harkokin nukiliyar, katsalandan ne ga harkokin hukumar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China