Hukumar ta bayyana haka ne bayan ta kammala nazarin tsaron nukiliyar kasar Sin da ta yi a karon farko, bisa bukatar hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar. IAEA ta kammala aikin nazarin da ya shafe kwanaki 10 ne a ranar Jumma'ar da ta gabata.
A rahotonta, hukumar ta ce kasar Sin ta dauki managartan matakan samar da ayarin tabbatar da tsaron nukiliyar da kiyaye dabarun tsaron, sannan ta taka muhimmiyar rawa wajen mara baya ga kawancen kare nukiliya a matakin yanki da ma duniya baki daya.
Shugaban sashen kula da kayayyaki da naurori na hukumar Muhammad Khaliq, ya ce yadda kasar Sin ke aiwatar da matakan kare makamashi da yadda take amfani da shawarwarin hukumar, alama ce dake nuna jajircewarta wajen tabbatar da tsaron nukiliya a ciki da wajen kasarta. (Fa'iza Mustapha)