in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi garambawul a asusun adana kudadenta a rukunin watanni hudun farko na bana
2017-06-30 10:28:41 cri

Kasar Sin ta rage adadin kudin da ta adana a asusunta, sannan ta yi garambawul game da yawan jarin kudadenta daga asusunta na mafi karamcin kudi zuwa asusunta mai yawan kudade.

An rage kudaden rarar asusun ajiyar kasar a cikin rukunin watanni hudun farko na wannan shekara zuwa dala biliyan 18.4 daga cikin adadin farko na dala biliyan 19, kamar yadda alkaluman da hukumar kula da musayar kudade ta kasar Sin (SAFE) ta bayyana.

Hukumar SAFE ta bayyana cewa jimillar jarin hada hadar kasar Sin ya tasamma dala trillion 6.5 zuwa karshen watan Maris, kana yawan jarinta na kasashen waje ya tasamma dala biliyan 1.3 da kuma dala biliyan 392.

Kudaden basukan kasar na kasashen ketare ya kai dala trillion 4.8.

SAFE tace, alkaluman sun nuna cewa, hada hadar kasuwanci ta cikin gida ya yi matukar tasiri wajen bunkasuwar zuba jari na kasashen ketare, kana masu zuba jari daga kasashen ketare na cigaba da kara zuba hannayen jarinsu a kasar Sin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China