in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta kara tura sojoji sama da dubu uku Afghanistan
2017-09-19 20:19:45 cri
Jiya Litinin, ministan tsaron Amurka, James Mattis ya tabbatar da cewa, Amurka za ta kara tura wasu dakarunta sama da dubu uku zuwa kasar Afghanistan, a wani yunkuri na inganta kwarewar sojojin gwamnatin Afghanistan a fanni yaki.

Tuni James Mattis ya sanya hannu kan wani umarni na kara tura sojojin.

A ranar 21 ga watan Agustan bana ne, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bullo da sabbin dabarun yaki a Afghanistan, inda ya ce, Amurka ba za ta janye dakarunta daga kasar ba, kana, sojojin Amurka za su dauki matakan soja bisa hakikanin halin da ake ciki, amma ba kamar yadda aka tsara tun farko ba.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China