in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren harkokin tsaron Amurka ya bada umurnin tura karin dakaru zuwa Afghanistan
2017-09-01 11:07:51 cri

Sakataren tsaron Amurka James Mattis, ya rattaba hannu kan umurnin tura karin dakaru zuwa Afghanistan.

James Mattis wanda ya ba da umurnin a jiya, ya shaidawa manema labarai cewa, ba zai yi wani karin bayani ba har sai ya gana da mambobin majalisar dokokin kasar cikin mako mai zuwa.

Sai dai, ya ce dakarun za su kunshi masu bada taimako da shawarwari da za su ba da dakarun Afghanistan damar yaki yadda ya kamata.

Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewa, kimanin dakaru 4,000 ne za a tura Afghanistan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China