Wani gidan telabijin din kasar Afghanistan ya ba da labarin cewa, ana samun tashin boma-boman ne a arewacin birnin Kabul. Sa'an nan wata majiya ta gayawa wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, wasu 'yan kunar bakin wake 3 su ne da hannu a kai hare-haren. An kai hare-haren ne, a lokacin da ake bikin jana'izar mutanen da suka rasa rayuka a zanga-zangar da ta gudana a birnin Kabul a ranar Jumma'ar da ta gabata.
Kafin haka, a ranar 31 ga watan Mayu, an kai hare-hare ta wasu motoci makare da boma-bomai a birnin Kabul, lamarin da ya yi sanadin rasa rayukan mutane a kalla 100, gami da raunatar wasu 600.
Ganin hakan ya sa jama'ar kasar damuwa sosai kan yanayin tsaro da ake ciki a hedkwatar kasar. Daga bisani a jiya Asabar, jama'ar birnin Kabul sun kaddamar da babbar zanga-zanga, inda suka bukaci gwamnatin kasar da ta dauki matakan da suka wajaba don tabbatar da kwanciyar hankali a kasar. Sai dai zanga-zangar a karshe ta rikide ta koma tarzoma, lamarin da ya haddasa mutuwar a kalla mutane 5.(Bello Wang)