Mai magana da yawun babban sakataren MDD Stephane Dujarric, ya ce mista Guterres abin da yake tunani shi ne, abu mafi muhimmanci shi ne, ya kamata kasashen duniya su hada kai don tallafawa kasar Afghanistan don ta lalibo hanyar warware rikicin kasar ta hanyar matakai na siyasa.
Amurka ta tura dakarunta kasar Afghanistan ne tun a shekarar 2001.
Trump ya bada sanarwa a ranar Litinin cewa ya yanke shawarar tura karin dakaru, saidai bai bayyana adadin da zai tura da kuma takamamman lokacin da zai tura karin dakarun ba, ko da yake a lokacin yakin neman zabensa, Trump ya sha nanata aniyar Amurkar na ficewa daga kasar Afghanistan. Wannan shine yaki mafi dadewa a tarihin Amurka.