kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa, wasu mahara ne suka kai hari masallacin mabiya darikar Shi'a dake unguwa ta 11 na arewacin birnin Kabul, a lokacin da jama'a da dama ke sallah.
Rahotannin sun ce mahara a kalla 4 ne suka kai harin, inda biyu daga cikinsu 'yan kunar bakin wake suka tada bam dake jikinsu a cikin masallacin, yayin da 'yan sanda suka harbi sauran biyun har lahira.
Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani da ya fitar da sanarwa a ranar, ya yi Allah wadai da harin, ya na mai bayyana shi a matsayin babban laifi ga jama'ar kasar .
Tuni dai Kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin harin. (Zainab)