Cikin wata sanarwa, kakakinsa Staphane Dujjaric, ya bayyana hari kan fararen hula a matsayin take hakkin dan adam da dokar jin kai ta duniya.
Harin ya zo ne kwana guda bayan wanda aka kai kan ofishin jakadanci Iraqi dake Kabul, inda 'yan asalin kasar ta Afghanistan 2 suka muta yayin da wani guda ya samu rauni.
Antonio Guterres ya kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gagagwa.
Har ila yau, ya jadadda goyon bayansa ga al'umma da gwamnatin Afghanistan. (Fa'iza Mustapha)