in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya jadadda tsare-tsaren sauya matsugunai a wani bangare na rage radadin talauci
2017-09-18 10:00:58 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jadadda tsare-tsaren sauya matsugunan jama'a daga wuraren da talauci ya yi wa katutu zuwa yankunan da suka ci gaba, a wani bangare na rage radadin talauci.

Cikin umarnin da ya rubuta ga taron rage fatara ta hanyar sauya matsugunan jama'a da aka kammala a jiya, Firaministan ya ce dole ne aikin ya kasance bisa tsari da adalci.

Da yake bayyana rage talauci ta hanyar sauya matsugunan jama'a a matsayin jigo wajen rage fatara da sake fasali a kasar, Li Keqiang ya ce ya kamata hukumomi su tabbatar da ingancin aikin tare da inganta kula da harkokin kudi.

Ya kuma bukaci hukumomi su taimakawa wadanda aka sauyawa muhallan, ta hanyar bunkasa masana'antu da kara musu hanyoyin samun kudin shiga, saboda a tabbatar da kowane iyali ya fita da kangin talauci bayan sauya muhallin.

A bana, kasar Sin ta shirya rage yawan al'ummarta dake fama da talauci da sama da miliyan 10, ciki har da miliyan 3.4 da za a sauyawa masugunai. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China