Firaministan na Sin ya bayyana hakan ne a Talatar nan 12 ga wata, yayin taron musayar ra'ayoyi tsakanin masu ruwa da tsaki, wanda aka yi wa lakabi da "1+6", taron da ya samu halartar kusoshin cibiyoyin tattalin arziki da dama.
Mr. Li ya ce duk da irin gibi da ake fuskanta a fannin cinikayyar kasuwannin duniya, Sin ta kaucewa takarar kudade da ka iya haifar da rage darajar kudinta domin fadada fitar da hajoji. Maimakon haka Sin ta mai da hankali ga shigo da karin hajoji. Hakan a cewarsa ya bunkasa damar zuba jari a kasar ga masu sha'awar hakan daga kasashen ketare.
Kaza lika sauye sauye da Sin ke aiwatarwa a wannan fannin, ya sa ta rage adadin hajoji da a baya aka hana shigarwa cikin kasar da kaso 65 bisa dari tun daga shekarar 2012.
Firaminista Li ya kuma bayyana cewa, Sin ta kafa yankunan cinikayya cikin 'yanci na gwaji har 11, a wani mataki na auna yanayin yadda hada hadar zuba jari ke gudana. Matakin zai kuma baiwa kasar damar tantance yanayin gudanar hada hadar cinikayya bisa doka, kuma cikin kyakkyawan yanayi.
Ya ce kasar Sin ta shige gaba, a jerin kasashe da ake burin zuba masu jari daga ketare. (Saminu Hassan)