in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen bunkasa harkar yawon shakatawa
2017-09-13 20:23:03 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar kasa da kasa, wajen bunkasa harkar yawon shakatawa. Mr. Li Keqiang wanda ya yi tsokacin cikin wata wasikar da ya aike ga taron dandalin bunkasa harkar yawon shakatawa ta kasa da kasa da ya gudana a jiya Talata, ya ce Sin za ta ci gaba da taka rawar gani wajen bunkasa wannan fanni.

Ya ce fannin na da fa'ida wajen samar da damammaki na ayyukan yi, da fadada ci gaban tattalin arzikin kasashe, tare da habaka musaya tsakanin kasashe daban daban.

Firaministan na Sin ya ce ana bukatar hadin gwiwa da aiki tare, wajen samar da daidaito, da ci gaba na bai daya a fannin raya harkar yawon bude ido. Kaza lika akwai bukatar gwamnatoci, da sassa masu zaman kansu, da sauran hukumomi, su shiga a dama da su wajen daukaka matsayin wannan fanni. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China