Wata sanarwa da aka fitar bayan taron, ta bayyana cewa, an cimma wannan shawara ce, bayan nasarar da aka samu a wasu manufofin yin gyare-gyare na gwaji kan yadda za a inganta wasu hukumomi da yanayin kasuwannin masana'antu da bangaren kirkire-kirkire, inda mahalartar taron suka goyi bayan cewa, lokacin ya yi da za a aiwatar da wadannan gyare-gyare a kasa baki daya.
Sanarwar ta kara da cewa, idan har ana son a karfafa gwiwar harkokin da suka shafi kirkire-kirkire, to, wajibi ne a tallafawa kanana da matsakaitan masana'antu da kudade. (Ibrahim Yaya)