in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya jaddada matsayin kasar Sin game da goyon bayan kirkire kirkire, da raya sana'o'i
2017-09-15 19:31:26 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana aniyar kasar Sin, ta ci gaba da goyon bayan dukkanin matakai da ka iya bunkasa sha'anin kirkire kirkire da daukaka sana'o'i. Ya ce Sin za ta dada kaimi a tafarkin ta, na samun ci gaba ta hanyar kere kere, da kirkirar sana'o'i masu alfanu.

Mr. Li wanda ya yi wannan tsokaci a Jumma'ar nan, gabanin shiga makon kasa na kirkire kirkire da bunkasa sana'o'i, ya kuma bayyana cewa wadannan fannoni, sun taka muhimmiyar rawa wajen fadada kasuwanni, da bunkasa fasahohin al'umma, tare da sauya alakar ci gaba, daga salo na gargajiya zuwa sabbin dabarun zamani.

Kaza lika a cewarsa, hakan na samar da damammaki dake haifar da daidaito, tare da fadada guraben ayyukan yi. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China