Mr. Li wanda ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci jami'ar ilimi da fasahar kere-kere ta Tianjian a nan kasar Sin, ya ce kamata ya yi a karfafa gwiwar yin kirkire-kirkire, yayin da ake kokarin aiwatar da dabarun bunkasa wannan harka, a hannu guda kuma a yi amfani da wadannan dabaru wajen samar da kayayyaki masu inganci.
Ya ce kasar Sin tana bukatar yaye karin kwarraru masu hazaka, ta yadda za a bunkasa sana'o'in hannu kana a karfafawa masana'antu daban-daban gwiwa samar da kayayyaki masu inganci, a wani mataki na bunkasa kayayyaki kirar kasar Sin.
A don haka ya yi kira da a kara kaimi wajen samar da yanayin da ya dace na mutunta malamai da martaba kimar ilimi, sannan a kara ingancin harkar ilimi ta yadda zai biya bukatun ci gaban tattalin arziki da jin dadin jama'ar kasar baki daya.
Firaminista Li dai ya kai wannan ziyara ce gabanin ranar malamai wadda ake bikinta a yau Lahadi 10 ga wannan wata na Satumba. (Ibrahim Yaya)