Jami'in sashen yada labarai na ofishin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD dake kasar Habasha, Axumite Gebre Egziabher ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, kasar Habasha ta karbi 'yan gudun hijira sama da dubu 851, wadanda a halin yanzu, suke zama a sansanonin 'yan gudun hijira 26 da aka kafa cikin jihohi 6 na kasar.
Haka kuma, hukumar na samar musu ruwan sha, abinci da kuma ayyukan kiwon lafiya da ilmi da dai sauransu.
Bugu da kari, Mr. Egziabher ya bayyana cewa, a halin yanzu, hukumar tana fuskantar kalubale da dama wajen gudanar da ayyukanta, musamman ma a fannin samun kudade.
Cikin watanni 8 da suka gabata, ta bukaci dallar Amurka miliyan 335 domin tallafawa 'yan gudun hijira dake zaune a Habasha, amma hukumar ba ta sami isashen taimako ba, inda ta samu dalla miliyan 252 kadai. (Maryam)