Songwe ta ce lokaci ya yi da kasashen nahiyar za su kara hada kan su kana su yi amfani da barazanar gibin da tsarin yin babakere ya haifar, sakamakon ficewar kasar Burtaniya daga kungiyar tarayyar Turai da kuma sabbin manufofin kasar Amurka na mayar da kanta saniyar ware.
Ya ce, muddin hukumar ECA tana fatan tunkarar kalubalen da nahiyar take fuskanta, ciki har da cin gajiyar albarkartun da Allah ya hore mata domin raya nahiyar, to ya zama wajibi a yi wa hukumomin nahiyar gyaran fuska.
A nasa jawabin firaminista Desalegn na kasar Habasha, ya ce ya yarda da kalaman jami'ar kungiyar ta ECA. Yana mai cewa, kamata ya yi hukumar ECA, da sauran takwarorinta, da hukumar kungiyar tarayyar Afirka (AUC) da bankin raya Afirka, su ci gaba da karfafa fatan nahiyar ta yadda za ta ci gaba da dagora da kanta. (Ibrahim Yaya)