Shugaban ofishin kula da hulda da yin cudanya na ma'aikatar harkokin ciniki ta kasar Habasha ya bayyanawa 'yan jarida a ranar 11 ga wata cewa, dalilin da ya sa aka samu bunkasuwar ciniki a tsakanin kasashen biyu shi ne, kafuwar dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2000, wanda ya samar da muhimmin dandali na hadin gwiwa da yin shawarwari a tsakanin Sin da Habasha har ma da nahiyar Afirka.
Bisa kididdigar da aka fitar, tun daga shekarar 2007 zuwa 2016, yawan kayayyakin da Habasha ta fitar zuwa kasar Sin yana karuwa da kashi 28.2 cikin 100 a kowace shekara, kana yawan kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa kasar Habasha ya karu daga kashi 24 cikin 100 zuwa kashi 33 cikin 100 bisa na yawansu da kasashen waje suka fitar zuwa kasar Habasha. (Zainab)