in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke wasu mutane 17 bisa zargin su da aikata kisan kiyashi
2017-08-21 11:17:59 cri

'Yan sandan kasar Habasha sun cafke wasu mutane 17, ciki hadda wasu tsaffin sojojin dake da kwarewa wajen sarrafa ababen fashewa, bisa zargin su da hannu a kaddamar da wasu hare hare a Bahir Dar, fadar mulkin jihar Amhara dake arewacin kasar.

Shugaban rundunar 'yan sandan birnin Walelign Dagnew, ya ce an kama mutanen da wasu gurneti masu tarin yawa, tare da kudi da ya kai kudin kasar birr 22,000, wadanda ake zaton za su yi amfani ne da su waje shirya hare haren ta'addanci.

Kamen dai na zuwa ne, a gabar da ake cika shekara guda da aukuwar wani dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaro da masu zanga zanga a Bahir Dar, garin dake da nisan kilomita 560 daga birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar ta Habasha, lamarin da ya sabbaba yamutsi da kisan mutane da dama.

A watan Agustan shekarar bara, masu zanga zanga daga kabilar Amhara sun gudanar da jerin gwano a Bahir Dar, domin nuna rashin amincewa da abun da suka kira mayar da su saniyar ware ta fuskar siyasa da tattalin arzikin kasar ta Habasha.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China