in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNDP ya yi alkawarin tallafawa kasar Habasha wajen inganta muhallin halittu
2017-08-25 12:41:13 cri

Hukumar kula da aikin raya cigaban kasashe na MDD (UNDP), ta yi alkawarin tallafawa kasar Habasha wajen gudanarwa da kuma kare muhallin halittun kasar.

Hukumar ta UNDP da gwamnatin kasar Habasha sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniya jiya Alhamis, a kokarin kara karfin kasar Habasha na kare abubuwa masu rai iri daban daban, ta hanyar gudanar da yankunan halittu yadda ya kamata da daukar matakan rage matsalolin farautar dabbobin daji da kuma yin fataucinsu ta haramtattun hanyoyi.

A lokacin sanya hannu kan yarjejeniyar, ma'aikatar kudi da tattalin arziki ta kasar Habasha ta bayyana cewa, ana saran wannan shiri zai bullo da matakan yaki da masu yin barazana ga muhallin halittu, kuma tuni an riga an ware kudi dalar Amurka miliyan 7.2 karkashin asusun kula da muhalli na duniya wato GEF, da kuma dala 200,000 daga hukumar UNDP, yayin da gwamnatin kasar Habasha za ta samar da dala miliyan 34.

Sanarwar ta ce, daga cikin maufofin shirin, akwai batun yaki da masu yin fataucin dabbobin daji ta haramtattun hanyoyi, musamman wajen tabbatar da kiyaye rayuwar giwaye wadanda a kullum adadinsu ke sake raguwa sakamakon yadda ake farautarsu da fataucin haurensu ta haramtattun hanyoyi.

Za'a aiwatar da shirin ne karkashin hadin gwiwa da hukumar kula da gandun daji na kasar Habasha (EWCA), wadda take da manyan gidajen adana namun daji 5 da suke da giwaye mafi yawa a kasar ta Habasha.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China