Yayin taron rabin shekara, game da nazarin halin da kasar ke ciki a wannan fanni, hukumar NDRMC ta ce adadin masu fama da yunwa a kasar zai iya karuwa daga mutum miliyan 7.8 zuwa miliyan 8.5 a nan gaba.
A farkon shekarar nan ta bana ne dai mahukuntan kasar ta Habasha suka bayyana cewa, mutane miliyan 5.6 na fama da kamfar abinci a kasar, kana bayan dan lokaci adadin ya karu zuwa mutum miliyan 7.2, kafin kuma a watan Yuni wannan adadi ya kai ga mutum miliyan 7.8. (Saminu Alhassan)