Wata sanarwar da ofishin watsa labarai na fadar shugaban kasar Habasha ya fitar, ta ce, a yayin ziyarar ana sa ran Mr Desalegn zai tattauna da shugaba Omar al-Bashir na Sudan kan yadda jagororin biyu za su nazarci hanyoyin karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da kuma batutuwan da suka shafi harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya dake shafar muradunsu.
Sanarwar ta kara da cewa, firaministan na Habasha zai kuma gana da takwaransa na kasar Sudan Bakri Hassan Saleh da kuma mataimakin shugaban kasar Sudan Hassabo Mohamed Abdul-Rahman.
An kuma tsara cewa, Mr Desalagn zai gabatar da lacca game da yankin kahon Afirka a babban dakin taron kawance dake birnin Khartoum, fadar mulkin kasar Sudan. Daga bisani kuma zai halarci liyafar al'adu da za a shirya masa da dare, baya ga ziyartar wasu kamfanoni da zai yi a kasar ta Sudan. (Ibrahim Yaya)