in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci Ingila da ta daina tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin
2017-09-15 19:52:18 cri

A Jumma'ar nan ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce kasar Sin na fatan kasar Ingila za ta daina kaddamar da rahoto kan yankin Hong Kong, ta kuma daina tsoma baki cikin harkokin Hong Kong.

A kwanan baya ne dai gwamnatin kasar Ingila, ta kaddamar da wani rahoto mai lakabin "batun Hong Kong a tsawon rabin shekara". Game da hakan, madam Hua Chunying ta amsa tambayar manema labaru, inda ta bayyana cewa, cikin shekaru 20 da mayar da yankin hannun kasar Sin, Hong Kong ta ci gaba da nuna fifikonta a sassa daban daban, ta kuma samu ci gaba sosai. Ta ce ana samun nasarar aiwatar da manufar "kasa daya, tsarin mulkin biyu" a yankin musamman na Hong Kong, wanda kowa yake iya gani.

Don haka jami'ar ta ce sam bai dace kasashen duniya su rika tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China