Xi Jinping ya gabatar da manyan batutuwa hudu game da ci gaba da aiwatar da manufar 'kasa daya da tsare-tsaren siysasa biyu' a yankin Hong Kong.
Da farko, ya ce ya kamata a kara fahimtar dangantaka tsakanin 'kasa daya' da 'tsarin siyasa biyu'. Sannan na biyu shi ne, gudanar da aiki bisa tsarin mulkin kasar Sin gami da babbar dokar yankin Hong Kong.
Sauran batutuwan sun hada da maida hankali kan neman ci gaba da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Hong Kong.
Xi Jinping ya kara da cewa, ya zama dole a tsaya ga manufar kasar Sin daya tak a duniya. Ya na mai cewa, Sam kasar Sin ba za ta amincewa da duk wani yunkuri na kawo barazana ga ikon mallakar yankinta ba.
Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, dole babban yankin kasar Sin ya kara tallafawa yankin Hong Kong, shi kuma bangaren Hong Kong, ya inganta karfinsa na neman ci gaba da kansa.(Murtala Zhang)