in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gama rangadinsa a yankin Hong Kong
2017-07-02 12:58:16 cri
A jiya Asabar, shugaban kasar Xi Jinping ya kammala rangadinsa a yankin Hong Kong na kasar Sin, sa'an nan ya koma birnin Beijing, fadar mulkin kasar.

Kafin haka, shugaban ya isa yankin Hong Kong ne a ranar Alhamis, inda ya fara rangadi a can. Yayin rangadinsa, shugaban kasar Sin ya halarci bikin murnar cikar yankin Hong Kong shekaru 20 bayan dawowarsa kasar Sin, da bikin kama aiki na gwamnatin yankin Hong Kong ta 5, da bikin liyafar da gwamnatin Hong Kong ta shirya don maraba da zuwan shugaban, haka kuma ya kalli bikin nuna fasahohin al'adu da aka shirya musamman ma domin murnar cika shekaru 20 bayan dawowar Hong Kong cikin kasar ta Sin.

Ban da haka kuma, shugaba Xi Jinping ya gana da wasu manyan kusoshin yankin Hong Kong, da suka hada da Tung Desem Waringin, mataimakin shugaban majalissar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin, da Leung Chun Ying, tsohon jagoran yankin Hong Kong, da Madam Carrie Lam Cheng Yuet-ngor, sabuwar jagorar yankin, gami da shugabannin hukumomin yankin Hong Kong masu kula da harkokin mulki, da tsara dokoki, da na gudanar da shari'a, da kuma wakilan yankin na sassa daban daban.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China