A yayin taron da ya gudana a ranar 21 ga wata a Washington D.C, babban birnin Amurka, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan dake jan hankulansu.
Kasashen biyu, sun kuma yarda da inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu, ta fuskar kyautata kwarewar kasashen Afirka, kan ayyukan kiyaye zaman lafiyar yankinsu, yayin hadin gwiwa da kasashen, wajen tabbatar da bukatunsu na karfafa ayyukan kiyaye zaman lafiya.
Bugu da kari, bangarorin biyu, sun kuma amince da karfafa ma'amala da hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin musayar bayanai dangane da yaki da ta'addanci da hana yaduwar harkokin ta'addanci ta yanar gizo da ta 'yan ta'adda tsakanin kasa da kasa, da kuma datse hanyoyinsu na samun kudade.
Har ila yau, kasar Sin da Amurka sun jaddada muhimmanci inganta hadin gwiwa wajen karfafa ayyukan kiwon lafiya na kasa da kasa, inda suka karfafawa juna gwiwar shiga ayyukan hukumar lafiya ta duniya WHO, sannan za su karfafa hadin gwiwa a fannin gwaje-gwajen magunguna da sauran harkokin lafiya.
Haka kuma, sun tsai da kudurin inganta ayyukan kiwon lafiya a kasashen Afirka. (Maryam)