Farfesa Lu Feng na sashen nazarin bunkasuwar kasa da kasa na jami'ar Beijing yana ganin cewa, shawarwarin wata alama ce dake nuna cewa, kasashen Sin da Amurka suna son warware matsalolinsu ta hanyar yin tattaunawa, kuma haka zai inganta dangantakar dake tsakaninsu.
Shugaban sashen nazarin tattalin arziki da siyasa na duniya na kwalejin nazarin kimiyya da zamantakewar al'umma na kasar Sin Zhang Yuyan ya bayyana cewa, a kokarin da ake yi na tinkarar kalubalen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta da farfado da ra'ayin ba da kariya ga harkokin ciniki, shawarwarin suna da babbar ma'ana ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Amurka a nan gaba, kana zai yi matukar tasiri ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Zainab)