Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya bukaci sassa masu ruwa da tsaki da su tattauna da juna, domin kawo karshen rashin jituwa game da batun nukiliya a zirin Korea.
Liu Jieyi, wanda ya yi wannan jan hankali yayin taron manema labarai, a daidai gabar da Sin ke kawo karshen jagorancin kwamitin tsaron MDD na karba-karba na watan Yuli, ya ce Sin ba za ta taba goyon bayan duk wani mataki na sabawa kudurorin kwamitin tsaron MDD ba, ciki hadda gwajin makamai masu linzami da Koriya ta Arewa ke gudanarwa.