in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin musamman na kasar Sin ya bayyana matsayin kasar Sin kan takunkumin da aka sanyawa Koriya ta Arewa
2017-08-06 13:25:53 cri

Dangane da sabon takunkumin da kwamitin sulhu na MDD ya sanyawa kasar Koriya ta Arewa, Liu Jieyi, wakilin musamman na kasar Sin a MDD ya bayyana a ranar 5 ga wata cewa, ainihin makasudin sanya wa Koriya ta Arewa takunkumi shi ne domin tsayawa tsayin daka kan tabbatar da hana shirin nukiliya a zirin Koriya, da warware batutuwa ta hanyar tattaunawa da shawarwari, da kin amincewa da barkewar yaki a zirin na Koriya.

Mista Liu ya kara da cewa, kudurin kwamitin sulhu mai lamba 2371 ya samu amincewar bai daya na kasashen duniya kan batun nukiliya na zirin Koriya, wanda ya hada da muhimman batutuwa 3, da farko, an kara sanyawa Koriya ta Arewa takunkumi saboda shirin nukiliyar Koriya ta Arewa. Na biyu, an kaucewa kawo illa ga harkokin tattalin arziki, hadin gwiwar tattalin arziki, samar da abinci, taimakon jin kai da sauran harkokin da ba a hana su ba. Na uku, an yi kira da a maido da shawarwari tsakanin bangarori 6, tare da yin alkawarin warware batun cikin ruwan sanyi, a siyasance kuma ta hanyar diplomasiyya. Kana, kudurin ya jaddada muhimmancin yadda sassa daban daban masu ruwa da tsaki za su sassauta zaman dar-dar da ake ciki.

Har ila yau, Liu Jieyi ya yi nuni da cewa, har kullum kasar Sin na rubanya kokarinta wajen tabbatar da kwance shirin nukiliya a zirin Koriya, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin. Kasar Sin tana fatan cewa, kasar Amurka za su cika alkawarinta a tsanake, wato ba ta nemi a sauya tsarin kasar Koriya ta Arewa ba, ba ta nemi a hambarar da mahukuntan Koriya ta Arewa ba, ba ta gaggauta sa azama kan dinkuwar zirin Koriya ba, kuma ba za ta tura sojoji su ketare layin da aka shata a tsakanin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China