A yayin ganawar tasu, Wang Yi ya ce, yanzu halin da ake ciki a zirin Koriya ya jawo hankalin duniya sosai, lamarin da ya kawo illa ga huldar dake tsakanin Sin da Koriya ta Arewa. Ya kuma jaddada cewa, yanzu rikici yana dab da barkewa, an kuma shiga muhimmin lokaci na tsai da kudurin komawa kan teburin shawarwari. Kasar Sin ta bukaci Koriya ta Arewa da kada ta ci gaba da sabawa kudurin kwamitin sulhu na MDD, yayin da Sin ta bukaci kasashen Amurka da Koriya ta Kudu da kada su ci gaba da ruruta wutar rikici a zirin Koriya. Dole ne sassa daban daban masu ruwa da tsaki su kai zuciya nesa, su fahimci alamu masu kyau da aka nuna a kwanan baya, su yi zabin da ya dace, a kokarin sauke nauyin dake wuyansu na kiyaye zaman lafiya a kasashensu da ma duniya baki daya.
A nasa bangaren, Ri Yong-ho ya sake nanata matsayin Koriya ta Arewa kan batun shirin nukiliyar zirin Koriya, ya kuma bayyana cewa, kasarsa na son ci gaba da tuntubar kasar Sin. (Tasallah Yuan)