Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar a jiya Alhamis, ta bayyana shirin ta na mayar da jakadanta kasar Iran, tare da burin sake bunkasa dangantakar sassan biyu a dukkanin fannoni. To sai dai sanarwar ba ta ayyana lokacin aiwatar da hakan ba.
A watan Janairun shekarar 2016 ne kasar Qatar ta janye jakadan ta daga Iran, bayan da Saudiyya ta yanke alaka da Iran din, bisa zargin mahukuntan kasar da gazawa wajen kare ofishin jakadancin ta dake birnin Tehran, da wani ofishin ta dake Mashahd, wanda hakan ya baiwa masu zanga zanga damar lalata ofisoshin.(Saminu Alhassan)