in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na shugaban kasar Sin ya halarci bikin rantsuwar kama aiki na shugaban kasar Iran
2017-08-07 10:17:41 cri
A jiya Lahadi ne manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma shugaban kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin He Lifeng, ya gana da shugaban kasar Iran Hassan Rouhani.

A yayin ganawar ta su, He Lifeng ya isar da sakon murnar lashe zabe daga shugaba Xi Jinping ga shugaba Rouhani, kana ya bayyana cewa, Sin tana fatan ci gaba da inganta mu'amala a tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu, da zurfafa hadin gwiwarsu bisa tsarin "ziri daya da hanya daya".

A nasa bangare, Rouhani ya bayyana cewa, kasar Iran na dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, da mai da kasar Sin muhimmiyar aminiya yayin da take gudanar da manufofin diplomasiyya. Kaza lika yana fatan ci gaba da hadin gwiwa tare da kasar Sin kan shawarar "ziri daya da hanya daya", da sa kaimi ga inganta hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, don amfanar jama'ar kasashen biyu yadda ya kamata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China