Wang Yun ya bayyana haka ne a yayin taro karo na 8, na kwamitin hadin kai game da yarjejeniyar nukiliyar Iran, wanda aka yi jiya Juma'a a birnin Vienna na kasar Austria tsakanin Iran da kasashe 6 da batun nukiliyar ya shafa, da suka hada da Amurka da Burtaniya da Faransa da Rasha da Sin da kuma Jamus.
A cewar Wang Yun, taron ya kasance muhimmin, la'akari da cikar yarjejeniya shekaru 2 da kulluwa.
Ya kuma jaddada cewa, yarjejeniyar na da ma'ana kwarai wajen inganta tsarin hana yaduwar makaman nukiliya, da tabbatar da zaman lafiya da zaman karko a yankin Gabas ta tsakiya, da kuma kiyaye ra'ayin kasancewar bangarori da dama.
Baya ga haka, Wang ya sanar da yadda ake gudanar da ayyukan gyara na'urar sarrafa ruwa mai nauyi ta Arak, yana mai cewa, kasar Sin za ta inganta ayyukan bisa yarjejeniyar da ra'ayin bai daya da bangarori daban daban suka cimma, don kara samun gagarumin ci gaba.
A yayin taron, bangaren Amurka ya bayyana cewa, zai cika alkawarin da ya dauka bisa yarjejeniyar, inda suma sauran bangarori suka jaddada na su goyon baya ga yarjejeniyar. (Bilkisu)