in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta tabbatar da faruwar harbin gargadi da dakarun Amurka suka gudanar
2017-07-26 10:22:44 cri
Rundunar tsaron kasar Iran ta IRGC, ta tabbatar da cewa, dakarun sojin ruwan Amurka sun yi harbin gargadi kan jirgin ruwan ta dake sintiri a kusa da gabar tekun Pasha.

IRGC ta ce da safiyar jiya Talata ne wannan lamari ya auku, wanda kuma a cewar rundunar hakan wani mataki ne na tsokanar fada.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan harbin na gargadi har karo biyu, jirgin sintirin na IRGC ya ci gaba da ayyukan sa, yayin da kuma jirgin ruwan na Amurka ya bar yankin.

Gidan talabijin na CNN ya rawaito cewa, jirgin ruwan na Iran ya matso ne kusa da na Amurka da nisan da bai wuce yadi 150 ba, wanda hakan ya sanya dakarun na Amurka gabatar da gargadi ta na'urar magana tsakanin su. Kuma kin sauraron hakan ya sanya harbin da ya biyo baya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China