in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta hana a ziyarci cibiyoyinta na soja
2017-08-28 09:54:33 cri
Babban mashawarci ga jagoran addinin Iran kan harkokin soja manjo janar Hassan Firouzabadi ya bayyana a jiya Lahadi cewa, cibiyoyin sojan kasar ba sa karkashin yarjejeniyar nukiliyar kasar da Iran din ta cimma da manyan kasashen duniyan nan shida shekaru biyu da suka gabata, a saboda haka ba za ta bari a ziyarci wadannan cibiyoyi ba.

Manjo janar Hassan ya kuma soki kalaman baya-bayan da jakadar Amurka a MDD Nikki Haley ta yi lokacin da ta ziyarci hedkwatar hukumar kula da harkokin makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) dake Vienna cewa, wani yunkuri ne Amurkar ke yi domin kawo nakaso ga yarjejeniyar da aka riga aka cimma.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ce dai Haley ta ce kasar Iran ta fito karara ta bayyana wa duniya cewa, ba za ta bari jami'an hukumar IAEA din su ziyarci cibiyoyin sojan nata ba. Amma kuma yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2015 ba ta bambance tsakanin cibiyoyin soja da wadanda ba na soja ba. Sai dai kuma manjo janar Hassan ya ce Haley 'yar koren Amurka ce dake kokarin kulla wata sabuwar makarkashiya kuma kalamanta babu kamshin gaskiya a ciki. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China