in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya jagoranci taro tsakanin kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki da kasashe masu tasowa
2017-09-05 14:47:18 cri

Yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron tattaunawa tsakanin kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki da kasashe masu tasowa a cibiyar taron kasa da kasa na birnin Xiamen, daga bisani ya gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya jaddada cewa, kamata ya yi sassa daban daban su kara karfafa hada kai da hadin gwiwa dake tsakanin su domin bullo da wani tsarin tattalin azikin duniya ba tare da rufa rufa ba, tare kuma da cimma ajandar samun dauwamammen ci gaba a fadin duniya nan da shekarar 2030, ta yadda a karshe za a kai ga kyautata tsari da kuma karuwar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.

Shugabannnin kasashen mambobin kungiyar BRICS da wasu shugabannin kasashen da suka hada da Masar da Guinea da Mexico da Tajikistan da Thailand da aka gayyata sun halarci taron, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan babban taken taron "kara zurfafa hadin gwiwa da sa kaimi kan bunkasuwa", musamman ma game da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, ta yadda za su cimma matsaya guda.

Shugaba Xi ya sanar a yayin bude taron cewa, yayin wani muhimmin jawabi mai taken "kara zurfafa hadin gwiwa domin samun moriyar juna, tare kuma da kara sa kaimi kan bunkasuwa tare., inda ya nuna cewa, yayin da ake gudanar da taron shugabannin kasashen BRICS, an gayyaci wasu sauran shugabannin kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki da kasashe masu tasowa domin su tattauna tare, hakan zai kara karfafa hada kai da hadin gwiwa dake tsakaninsu, tare kuma da kara kyautata tsarin hadin gwiwa dake tsakanin kasashen BRICS.

Bayan taron tattaunawar, kasar Sin ta bayar da sanarwar shugaba, inda ta yi bayani kan ra'ayi daya da aka cimma yayin taron, tare kuma da nuna wa al'ummomin kasashen duniya aniyya da imani na sassa daban daban yayin da suke aiwatar da ajandar samun dauwamammen ci gaba, kana sanarwar ta jaddada cewa, kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki da kasashe masu tasowa za su gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu yadda ya kamata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China