in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayyana sakamakon zabe a Angola
2017-09-07 10:23:31 cri
Da misalin karfe 6 na daren jiya Laraba ne hukumar zaben kasar Angola, ya sanar da sakamakon babban zaben majalissar dokokin kasar da aka yi a ranar 23 ga watan da ya gabata.

Jam'iyyar MPLA mai mulkin kasar ce dai ta lashe zaben da aka kada. Sa'an nan dan takarar jam'iyyar, kana ministan harkokin tsaron kasar Joao Lourenc ya kasance zababben shugaban kasar mai jiran gado. Mr. Lourenc ya zamo sabon shugaban kasar na farko cikin shekaru 38 da suka gataba.

Joao Lourenc mai shekaru 63, ya fara aiki a matsayin ministan tsaron kasar Angola a shekarar 2015, sa'an nan, aka zabe shi a matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar MPLA a watan Agusta na shekarar 2016.

Bayan bayyana sakamakon zaben, ya ce, gwamnatinsa za ta dukufa wajen samar wa al'ummomin kasar kyakkyawar makoma.

Shugaban kasar mai barin gado Jose Eduardo Dos Santos, ya kasance shugaban kasar tun daga shekarar 1979. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China