Tawagar karkashin jagorancin tsohon firaministan Cape Verde Jose Maria Neves, ta kunshi jami'an sa ido 40 daga kwamitin wakilan din-din-din da majalisar dokoki na tarayyar da hukumomin kula da zabe da kungiyoyin al'umma da kuma malamai.
Aikin tawagar shi ne, bada sahihin rahoto ba tare da nuna fifiko ba, ko kuma tantance ingancin babban zaben Angola, ciki har da yadda gudanar da zaben ta kai matakin inganci na nahiyar da kasashen ketare.
Har ila yau, tawagar za ta ba da shawarwari kan yadda za a inganta zabuka masu zuwa, la'akari da abubuwan da za ta gano. (Fa'iza Mustapha)