Babbar jam'iyyar adawa ta Angola (UNITA) ta sa kafa ta shure sakamakon wucin gadi na babban zaben kasar na ranar Laraban da ta gabata da hukumar zaben kasar ta sanar a jiya Alhamis.
Wakilin jam'iyyar Jose Pedro Catchiungo ya bayyana a yau Jumma'a cewa, hukumar zaben ta yi kuskure kuma sakamakon da ta bayyana babu gaskiya a cikinsa.
Sakamakon babban zaben kasar na shekarar 2017 da hukumar zaben kasar ta bayyana dai na nuna cewa, jam'iyyar MPLA mai mulki ce ke kan gaba da kaso 64.57 cikin 100 na kuri'un da aka kada. (Ibrahim)