Jam'iyya mai mulkin kasar ta MPLA ta lashe zaben da kaso 61 na kuri'un da aka kada, bayan an kidaya kaso 98 na kuri'un.
Wata sanarwar da babbar jam'iyyar adawa ta kasar UNITA ta wallafa jiya a shafinta na yanar gizo ta ruwaito cewa, 7 daga cikin mambobin kwamitin gudanarwar hukumar zaben kasar, sun ce ba su ga wani sako mai kunshe da bayanan kuri'u da aka kada a rumfunan zabe da har za a yi amfani da shi a matsayin sakamako ba.
A cewar jam'iyyar adawa ta biyu a kasar Cosa-CE, hukumar zaben ta sanar da sakamakon da ba su da kwakkwaran tushe daga larduna, tana mai cewa ba a san asalin inda aka samo sakamakon ba.
Shugaban Jam'iyyar UNITA Isias Samakuva ya shaidawa manema labarai a ranar Asabar da ta gabata cewa, Angola ba ta da zababben shugaban kasa, saboda sakamakon da hukumar zaben ta fitar ba shi da sahihanci. (Fa'iza Msutapha)