Sakamakon farko da hukumar zaben kasar Angola CNE ta fitar a jiya Alhamis ya nuna cewa, jam'iyyar MPLA mai mulki a kasar ce a kan gaba, kuma dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar Joao Lourenco yana gab da lashe zaben bayan da ya samu kashi 64.5 cikin 100.
Jami'yyar UNITA ce take bi mata baya da kashi 24.4 cikin 100, sai kuma jami'yyar CASA-CE da ta samu kashi 8.56 bisa 100.
Kuri'a sama da miliyan 5.9 ne aka tantance su, adadin da ya kai kashi 63.74 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada a zaben.
Kwarya-kwaryar sakamakon na zaben ya nuna cewa, mutane sama da miliyan 1.3 ne suka kauracewa zaben a duk fadin kasar, adadin da ya kai kashi 18.64 cikin 100.(Ahmad Fagam)