A yayin taron manema labaru da aka yi a yau Talata, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce, shugabannin kasashen BRICS sun amince da cewa, kasashen nan 5 mambobin kungiyar BRICS na da dogon tarihi, da nagartattun al'adu, wadanda dukiya ke darajantawa, kuma ya zama wajibi a ci gaba da darajta su sosai.
Ya ce a kullum, kasashen BRICS za su goyi bayan kafa tsarin mu'amala da hadin gwiwa ta fuskar al'adu a tsakaninsu, a kokarin kara fahimtar juna tsakanin al'ummunsu da zumuncinsu, tare da sanya tunanin raya huldar abokantaka a cikin zukatansu.(Tasallah)