A cewar Kamath, kasar Sin ta kasance ta farko cikin mambobin kungiyar da ta samar da kudin ajiya a bankin. Za a yi amfani da kudaden ne wajen samar da yanayin da ya dace na gudanar da aikin bankin, ta yadda za a samu nasarori, da bullo da shirye-shiryen inganta dangantakar abokantaka tsakanin kasa da kasa, da kuma gudanar da ayyukan yin bincike da dai sauransu.
Kamath ya bayyana cewa, tun bayan kafuwar sabon bankin raya kasa na BRICS, ya zuwa an amince da ayyukan ba da rancen kudi guda 11, wadanda suka kai dalar biliyan 3 da wani abu. (Bilkisu)