in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#BRICS# Xi Jinping: bude sabbin kyawawan shekaru 10 ga hadin gwiwar kasashen BRICS
2017-09-05 13:26:36 cri
A yayin wani taro na manema labaru da ya gudana da tsakar ranar Talatar nan 5 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana sakamakon da aka samu, a yayin taron ganawa tsakanin shugabannin kasashen BRICS, da taron tattaunawa tsakanin kasashen da tattalin arzikinsu ke samu saurin bunkasuwa, da kasashe masu tasowa.

Xi Jinping ya bayyana cewa, shugabannin kasashe daban daban sun daura aniyar mayar da taron Xiamen matsayin sabon mafari, na kafa wata huldar abokantaka bisa manya tsare-tsare irin na kud da kud daga dukkan fannoni, ta yadda za su iya bude sabbin kyawawan shekaru 10 masu zuwa ga hadin gwiwar kasashen kungiyar BRICS. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China