in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Masar Abdel-Fattah el-Sisi
2017-09-05 11:44:39 cri
A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban kasar Masar Abdel-Fattah el-Sisi a birnin Xiamen dake gabashin kasar Sin.

A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya yi maraba da zuwan shugaba Abdel Fattah el-Sisi kasar Sin, domin halartar taron tattaunawa a tsakanin kasashe da tattalin arzikinsu ke samu saurin bunkasuwa, da kasashe masu tasowa. Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin na mai da hankali sosai kan kokarin bunkasa huldar dake tsakaninta da kasar Masar. Don haka ya ce ya kamata kasashen biyu, su nazarci shirye-shiryen neman ci gaban su, domin kokarin samar da kayayyakin more rayuwa, da yin hadin gwiwa a fannin makamashi, ta yadda za a iya mai da kasar Masar wata muhimmiyar kasa bisa shawarar "ziri daya da hanyar daya" da kasar Sin ta gabatar. Yanzu haka dai bangaren Sin na nuna goyon baya ga kamfanonin kasar Sin, wajen zuba jari, da kuma bunkasa masana'antu a kasar Masar. Sannan yana fatan bangarorin biyu za su kara yin hadin gwiwa a fannonin yakar ayyukan ta'addanci da tsaro, da kuma kara daidaita matsayinsu kan wasu al'amura na kasa da kasa, da na shiyya-shiyya.

A nasa bangaren, shugaba El-Sisi ya bayyana cewa, bangaren Masar ya amince da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta kasar Sin. Tana kuma fatan kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin zuba jari, da samar da kayayyakin more rayuwa da dai makamatansu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China