in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da takwaransa na Guinee Alpha Condé
2017-09-05 11:32:50 cri
A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Guinee Alpha Condé, wanda ke halartar taron tattaunawa a tsakanin kasashe da tattalin arzikinsu ke samu saurin bunkasuwa, da kasashe masu tasowa.

A yayin ganawar Shugaba Xi ya nuna cewa, Sin da kasashen Afirka su kasance abokai da 'yan uwan juna. Kasar Sin ta gabatar da sahihan manufofi ga kasashen Afirka, da nuna ra'ayi na gaskiya a fannin da'a, da cin moriya da nufin hada kan ci gaban Afirka, da tallafawa ci gaban nahiyar, ta yadda za a iya tabbatar da samu nasara da bunkasuwa tare.

A cewar shugaba Xi, kasar Sin na maraba da kasashen Afirka, ciki har da Guinee don halartar shirin 'Ziri daya da hanya daya', hakan wata hanya ce ta kara samar da gajiya ga jama'ar Sin da na kasashen Afirka.

A nasa bangare, shugaba Condé ya bayyana cewa, kasashen Afirka na jinjinawa manufar da Sin ke goyon baya, ta girmama kasashen Afirka ta yadda za su warware matsalolinsu da kansu. Kana yana fatan karfafa hadin kai a tsakanin kasashen Afirka da Sin, tare kuma da karfafa tattaunawa da hadin kai a tsakanin kungiyar AU da Sin kan harkokin kasa da kasa.

Bayan ganawar, a idanun shugabannin biyu, an sa hannu kan jerin takardun hadin kai a tsakanin bangarorin biyu a fannonin fasahar tattalin arziki, da sauyin yanayi, da kuma aikin jinya da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China